Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Emmerson Mnangawa ya lashe zaben Zimbabwe

Hukumar zabe a kasar Zimbabwe ta bayyana shugaban kasa Emmerson Mnangawa Dambudzo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar, irin sa na farko bayan kawo karshen mulkin shugaba Robert Mugabe.

Emmerson Mnangagwa Shugaban kasar Zimbabwe
Emmerson Mnangagwa Shugaban kasar Zimbabwe Tafadzwa Ufumeli/via REUTERS
Talla

Shugabar hukumar zaben, Priscilia Chigumba ta gabatar da sakamakon zaben wanda ya nuna cewar zababben shugaban ya samu kuri’u sama da kashi 50.

Chamisa Nelson daga kawancen MDC, ya samu kuri’u 2,147, 436 wanda shine kashi 44.3 na kuri’un da aka kada.

Mnangagwa Emmerson Dambudzo na Jam’iyyar ZANU PF ya samu kuri’u 2,460, 463 wanda shine kahsi 50.8.

Shugabar hukumar zaben kasar Priscilia Makanyara Chigumba, a karkashin sashe na 110, sakin layi na 3, sakin layi 6, sakin layi na 2, ta jadadda cewar kuri’un da Emmerson Mnangagwa Dambudzo ya samu na Jam’iyyar ZANU PF sun zarce rabin kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa.

Saboda haka Mannagawa Emmerson Dambudzo na Jam’iyyar ZANU PF ya zama zababen shugaban kasar Jamhuriyar Zimbabwe daga yau 3 ga watan Agusta na shekarar 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.