Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Chamisa ya yi fatali da sakamakon zaben shugabancin Zimbabwe

Dan takarar jam’iyyar MDC mai adawa a zaben Zimbabwe Nelson Chamisa, ya yi watsi da sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar da ke bayyana Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya yi nasara.

Emmerson Mnangagwa (a hagu) Nelson Chalisa (a dama).
Emmerson Mnangagwa (a hagu) Nelson Chalisa (a dama). Jekesai NJIKIZANA, Ahmed OULD MOHAMED OULD ELHADJ / AFP
Talla

A taron manema labaran da ya gabatar a tsakiyar ranar yau juma’a. Chamisa, ya bayyana sakamakon da hukumar zaben kasar ZEC ta fitar da cewa ba ya da wani tasiri, inda ya yi zargin cewa an tafka magudi domin bai wa jam’iyyar da ke kan karagar mulki damar cigaba da jagorantar kasar.

Hukumar zaben dai ta bayyana Mnangagwa dan takarar Zanu-PF da cewa ya samu kashi 50.8% yayin da Chamisa na jam’iyyar MDC ya samu 44.3% na kuri’un da aka kada a zaben wanda aka yi ranar litinin da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.