Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mutane 6 sun mutu a rana ta biyu da fara Zanga-zangar zabe a Zimbabwe

Adadin mutanen da Jami’an tsaro suka harbe har lahira a zanga-zangar adawa da yunkurin magudin zabe a Zimbabwe ya kai mutane 6 maimakon 3 da gwamnatin kasar ta sanar a jiya.Sanarwar da Jami’an ‘yan sanda suka fitar ta ce akwai kuma tarin mutane da suka jikkata a zanga-zangar wadanda yanzu haka su ke ci gaba da karbar kulawar gaggawa a Asibiti.

Ko a yammacin nan ma sai da Matashi Nelson Chamisa ya bayyana gaban yan jaridu a Harare inda ya sake jaddada cewa shi ne fa ya lashe zaben, tare da zargin hukumar zabe da kokarin murde sakamakon zaben da ba a bayyana ba.
Ko a yammacin nan ma sai da Matashi Nelson Chamisa ya bayyana gaban yan jaridu a Harare inda ya sake jaddada cewa shi ne fa ya lashe zaben, tare da zargin hukumar zabe da kokarin murde sakamakon zaben da ba a bayyana ba. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

A jiya ne dai gwamnatin ta Zimbabwe ta yi umarnin baza jami'an soji a sassan da mutane suka taru don gudanar da zanga-zangar zargin magudin zabe, matakin da ya sanya jami'an bude wuta tare da hallaka akalla mutane 3.

Tuni dai shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya bukaci kwantar da hankali a dai dai lokacin da jami’an soji ke ci gaba da sinturin tsaro kan titunan Harare.

Kawo yanzu dai hukumar zaben kasar ta gaza bayyana sakamakon zaben ko da dai ta tabbatar da cewa a daren yau alhamis za ta fitar da shi, inda ta bukaci al'umma su nuna halin dattako da hakuri.

Gwamnatin kasar ta Zimbabwe ta ce tana kokarin ganin ta shawo kan matsalar da ke tsakaninta da yan adawa musamman shugabansu Nelson Chamisa, da ke ci gaba da ikirarin samun nasara, matakin da ake ganin shi ke kara rura wutar zanga-zangar.

Ko a yammacin nan ma sai da Matashi Nelson Chamisa ya bayyana gaban yan jaridu a Harare inda ya sake jaddada cewa shi ne fa ya lashe zaben, tare da zargin hukumar zabe da kokarin murde sakamakon zaben da ba a bayyana ba.

Akwai dai kyakkyawan zaton zaben na Zimbabwe zai bude sabon babi ga tarihin siyasar kasar wadda Jam'iyya guda ke mulka tun 1980 tsawon shekaru 37.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.