Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Zanu PF na kan gaba da yawan kujerun majalisar dokoki a Zimbabwe

Jam’iyar da ke mulkin kasar Zimbabwe tun cikin shekarar 1980, Zanu-PF, ta samu rinjayen farko na lashe kujerun majalisar dokoki, kamar yadda sakamakon wucin gadi da hukumar zaben kasar ta fitar a yau laraba ya nunar, a yayin da kidayar kuri’un zaben shugabancin kasar da ake zargin an tafka magudi a cikinsa ke ci gaba da gudana.

A wata rumfar zabe a Chegutu, dake  Zimbabwe,30 yuli  2018.
A wata rumfar zabe a Chegutu, dake Zimbabwe,30 yuli 2018. REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

A yau laraba ne dai yan kallon kungiyar tarayyar turai za su bada sanarwa kan sahihancin zabubbukan shugancin kasar, yan majalisar dokoki da kuma na kananan hukumomin da aka gudanar a ranar litanin da ta gabata a kasar ta Zimbabwe, irinsa na farko tun bayan kawo karshen mulkin Robert Mugabe dan shekaru 94 a watan november bara, bayan share tsawon shekaru 37 kan kujerar mulki

Zaben farkon da aka gudanar bayan Mugabe ya hadu da matsalolin magudi da tashe tashen hankulla. Magajin Mugabe tsohon na hannun damarsa Emmerson Mnangagwa, dake son raba hanya da tsohon maigidan na shi, ya dau alkawalin gudanar da zaben cikin adalci, kwanciyar hankali da kuma haske.

Wannan kuma domin nuna wa duniya cewa, da gaske yake yi ne, ya sa ya gayyato yan kallo daga kasashen yammaci domin zura ido a zaben, irinsa na farko a shekaru 16 da suka gabata.

A jiya laraba hukumar zaben kasar ta (ZEC) ta fitar da sakamakon wucin gadin na yan majalisar dokoki yankuna 153 daga cikin 210 da aka yi zabe a kasar, inda ta ce jam’iyar Zanu-PF ce ta lashe yawan kujeru 110 a yayin da ta MDC mai adawa ke da kujeru 41.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.