An kara samun barkewar Ebola a Jamhuriyar Congo
Gwamnatin Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo ta ce yanzu haka kasar na fuskantar barazanar barkewar wata sabuwar cutar Ebola, mako guda bayan kasar ta bayyana kawo karshen cutar wanda ta lakume rayukan mutane 33.
Wallafawa ranar:
Gwamnan Arewacin Kivu, Julien Paluku ya ce an samu sabuwar cutar ce a yankin sa, kusa da iyakar Uganda, inda ya bukaci al’ummar Yankin da su kwantar da hankalin su.
Ya zuwa yanzu hukumomi ba suyi cikaken bayani kan mutane nawa ne suka kamu da cutar ba, sai dai ma’aikatar lafiya ta ce akalla mutane 25 sun kamu da zazzabi mai zafi kusa da garin Beni, kuma an dauki jinin su domin gudanar da bincike a Kinshasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu