Isa ga babban shafi
Najeriya-Amnesty

'Yan bindiga sun kwace iko da wasu sassan Zamfara - Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce 'Yan bindiga sun karbe iko da kauyukan Jihar Zamfara da ke Najeriya, inda su ke cin karen su ba bu babbaka.Sanarwar kungiyar tace akalla mutane 371 'yan bindigar suka kashe a cikin watanni shida da suka gabata.

Ko a jiya shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin aikewa da karin jami'an tsaro hade da jiragen yaki jihar ta Zamfara da ke fama da rikici.
Ko a jiya shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin aikewa da karin jami'an tsaro hade da jiragen yaki jihar ta Zamfara da ke fama da rikici. Daily Trust
Talla

Sanarwar da kungiyar Amnesty International ta bayar ta ce harkokin tsaro sun tabarbare a Jihar Zamfara da ke Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, inda a kowacce rana Yan bindiga ke kasha mutane ba tare da kaukautawa ba da kuma garkuwa da wasu domin karbar diyya.

Kungiyar tace wadanan hare hare sun tilastawa dubban mutane tserewa daga gidajen su sakamakon tahsin hankalin da ya samo assail daga rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Daraktan kungiyar a Najeriya, Osai Ojigbo ta ce rashin daukar matakan da suka dace ya sa mazauna yankin sun rasa madafa, abinda ya sa aka kasha daruruwan su a cikin shekaru 2 da suka gabata.

Jami’ar ta ce lokacin da suka ziyarci Yankin, mazauna kauyukan sun shaida musu cewar sau tari idan sun samu sako daga Yan bindigan cewar suna tafe, su kan shaidawa hukumomi amma basa daukar matakan kare su.

Kungiyar ta ce a ranar 27 ga watan jiya, mutane 42 aka kasha a kauyukan Mashema da Kwashabawa da Birane dake karamar hukumar Zurmi, yayin da mutane 18,000 suka rasa matsugunin su, kana washe kari aka sake kashe wasu 15.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara tura sojoji 1,000 da kuma jiragen yaki domin shawo kan matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.