Isa ga babban shafi

Bukola Saraki ya sauya sheka daga Jam'iyyar APC zuwa PDP

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Sanata Abubakar Bukola Saraki ya sanar da ficewarsa daga Jam'iyyar APC mai mulkin kasar tare da komawa tsohuwar Jam'iyyarsa ta PDP.

Yanzu haka dai Jam'iyyar APC ta shugaba Muhammadu Buhari na kokarin rasa rinjaye a majalisun kasar dama sassa daban daban a dai dai lokacin babban zabe na 2019 ke tunkarowa.
Yanzu haka dai Jam'iyyar APC ta shugaba Muhammadu Buhari na kokarin rasa rinjaye a majalisun kasar dama sassa daban daban a dai dai lokacin babban zabe na 2019 ke tunkarowa. punch
Talla

Saraki wanda ya sanar da ficewar ta sa a yau Talata ya ce hakan ya biyo bayan dogon nazarin da ya yi da kuma tuntubar dubban magoya baya kan matakin da ya kamata ya dauka.

Ficewarta ta saraki ta zo a dai dai lokacin da shima gwamnan jihar Kwara AbdulFatah Ahmed da kakakin jam'iyyar Bolaji Abdullahi ke sanar da sauya sheka daga APC zuwa PDP babbar Jam'iyyar adawa a Najeriya.

Ko a makon da ya gabata ma akalla mambobin majalisar dattijan kasar 15 ne suka sauya sheka daga APC zuwa PDP yayinda tsirarun mambobi daga jihohin kasar ke ci gaba da sauya sheka.

Yanzu haka dai Jam'iyyar APC ta shugaba Muhammadu Buhari na kokarin rasa rinjaye a majalisun kasar dama sassa daban daban a dai dai lokacin babban zabe na 2019 ke tunkarowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.