Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mugabe ya bukaci a kayar da jam'iyyarsa a zaben shugaban kasa

Tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe, ya yi kira ga al'ummar kasar da su kayar da jam'iyyarsa ta ZANU-PF a zaben shugabancin kasar da aka soma.

Masu zabe a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, yayinda suke shirin fara kada kuri'a a zaben shugabancin kasar. 30 ga watan Yuli, 2018.
Masu zabe a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, yayinda suke shirin fara kada kuri'a a zaben shugabancin kasar. 30 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Mugabe ya yi kiran ne yayin jawabin da ya gabatar ta wata kafar Talabijin da ke kasar ta Zimbabwe.

00:53

Robert Mugabe ya bukaci a kayar da jam'iyyarsa a zaben shugabancin kasar

Salissou Hamissou

Yau Litinin, 30 ga watan Yuli na 2018, ake gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a Zimbabwe, karo na farko tun bayan kifar da gwamnatin Robert Mugabe wanda ya jagoranci kasar tsawon shekaru 37.

‘Yan takara biyu ne ke shirin fafatawa da juna a zaben na yau, wato Emmerson Mnagagwa mai shekaru 75 a duniya wanda kuma ya kwace mulki daga hannun Robert Mugabe da kuma Nelson Chamisa matashin dan siyasa mai shekaru 40 a duniya.

Kafin wannan zabe dai, hasashe ya yi nuni da cewa idan har ma dan takarar jam’iyya mai mulki zai yi nasara a zaben, to ba za a samu wata tazara mai yawa a tsakaninsu ba, yayin da wasu ke hasashen cewa za a iya zuwa zagaye na biyu a ranar 8 ga watan gobe kafin fitar da gwani a tsakaninsu.

Jajibirin wannan zabe dai tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, ya ce ba zai jefa wa dan takarar jam’iyyarsa ta ZANU-PF wato Emmerson Mnangagwa kuri’arsa ba, inda ya yi kira ga sauran al’ummar kasar da su kada kuri’ar kayar da gwamnatinsa.

Mugabe ya ce, ba zai jefa kuri’arsa ga wadanda suka cutar da shi ba tare da bayyana shugabancin Mnangagwa a matsayin wanda ba ya da halasci, abin da ke nufin cewa zai mara wa dan takarar jam’iyyar adawa ta MDC Nelson Chamisa ne a zaben na yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.