Isa ga babban shafi
Mali

Zaben Mali zai gudana cikin tsauraran matakan tsaro

Al’ummar kasar Mali na ci gaba da shirye-shiryen kada kuri’a a zaben shugabancin kasar a gobe Lahadi cikin tsauraran matakan tsaro

Wasu daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya da ke sintiri a Bamako, babban birnin kasar Mali, yayin da ake shirin gudanar da zabe a ranar Lahadi, 29 ga watan Yuli, 2018.
Wasu daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya da ke sintiri a Bamako, babban birnin kasar Mali, yayin da ake shirin gudanar da zabe a ranar Lahadi, 29 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Luc Gnago
Talla

Jami’an tsaro masu yawan gaske da suka hada da na kasar da kuma dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya ke gudanar da sintiri a sassan kasar domin tabbatar da cikakken tsaro yayin gudanar da zabe.

Akalla mutane miliyan takwas hukumar zaben kasar ta yi wa rijistar cancantar kada kuri’a a zaben wanda za a soma shi daga karfe 8 na safe agogon GMT zuwa 6 na yammacin ranar ta Lahadi.

Shugaban kasar Ibrahim Boubakar Keita da ke neman wa’adi na biyu, na fuskantar ‘yan takara sama da 24, sai dai daga cikinsu, ana ganin Souma’ila Cisse ne ke da karfin magoya bayan, da ya bashi dama zama abokin hamayya mafi girma ga shugaban kasar mai ci.

Zaben na Mali ya zo ne dai dai lokacin da kasar ke kokarin shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi sassanta, kama daga na ta’adda da kuma rikicin kabilanci, musamman a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar, tsakanin mafarautan kabilun Bambara da Dogon kuma Fulani.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu karuwar yawan wadanda suka rasa rayukansu, a rikicin kabilanci a yankin tsakiyar kasar ta Mali, daga 3 zuwa akalla mutane 17, sakamakon harin da wasu mafarauta da ake kyautata zaton sun fito ne daga kabilun Dogon da Bambara suka kai, kan kauyen Somena.

Shugaban kungiyar Fulani ta Tapital Pulaaku na kasar ta Mali, Abdoul Aziz Diallo ne ya bada tabbacin alkalumman.

A ranar 17 ga watan Yuni na 2018, hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya ta ce akalla mutane 289 ne suka rasa rayukansu sakamkon rikicin kabilanci a Mali daga farkon wannan shekara zuwa yanzu, kuma kashi 77 na tashin hankali na aukuwa ne a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.