Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Zaben shugabancin Zimbabwe na farko zai gudana bayan shudewar Mugabe

A ranar litani 30 ga wannan wata na Yuli ne, al’ummar kasar Zimbabwe ke kada kuri’ar zaben shugabancin kasar da na majalisar dokoki karo na farko tun bayan kawo karshen mulkin stsohon shugaban kasar Robert Mugabe, da sojoji da jam’iyarsa ta Zanu PF suka tilastawa yin murabus a 2017, bayan shere shekaru 37 kan kujerar mulkin kasar.

shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa , 23.06.2018
shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa , 23.06.2018 Tafadzwa Ufumeli/via REUTERS
Talla

Bayan kammala yakin neman zaben da aka gudanar a cikin tsanaki, tsakanin yan takarar Shugabancin kasar 23 a kasar da tattalin arzikinta ke kan farfadowa.

Ana ganin cewa zaben na ranar litanin zai iya samun sauyin shugabanci a kasar ta Zimbabwe, inda za a kara tsakanin shugaban rikon kwaryar kasar, haka kuma tsohon mataimakin shugaba Robert Mugabe, Emmerson Mnangagwa mai shekaru 75 da haihuwa, da sauran yan takarar adawa da ake ganin suna kankankan da juna.

Shi dai wannan zabe zai iya zama zakaran gwajin dafi ga makomar kasar ta Zimbabwe da ta share tsawon lokaci tana fama da matsalolin siyasa da na tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.