Mnangagwa ya yi wa jar fata alkawarin ba su kariya
Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da ke neman kuri’ar jama’a a zaben da za a yi ranar 30 ga wannan wata na yuli, ya yi wa har fatar kasar alkawarin cewa ba wanda zai sake masu gonaki matukar dai ya yi nasara a zaben.
Wallafawa ranar:
Mnagagwa wanda ke gabatar da jawabi ga wakilan jar fatar kasar a birnin Harare safiyar yau asabar, ya ce bai kamata su nuna wata fargaba dangane da makomarsu a wannan kasa ba.
A lokacin mulkin Robert Mugabe, gwamnati ta kaddamar da wani gagarumin shiri inda aka kwace dimbin filayen noma daga hannun jar fata tsiraru domin danka su a hannu bakake masu rinjaye, to sai dai matakin ya haddasa koma-baya ga sha’anin noma a wannan kasa, lura da yadda aka mika filayen a hannu wadanda ba su da niyar gudanar da aikin gona.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu