Isa ga babban shafi
Gambia

Gwamnatin Gambia ta mayar da martani zuwa Jammeh

Gwamnatin kasar Gambia tayi Allah wadai da barazanar tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh na cewar yana shirin komawa gida daga Equatorial Guinea, inda ya samu mafakar siyasa yanzu haka.

Adama Barrow Shugaban kasar Gambia
Adama Barrow Shugaban kasar Gambia REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Hirar da akayi da tsohon shugaban da aka nada ta waya, ake ta kuma yadawa ta kafar sada zumunta, ta ruwaito Jammeh na cewa babu wani mahaluki da zai hana shi komawa Gambia.

Gwamnati mai ci ta bayyana kalaman tsohon shugaban a matsayin yadda ya matsu ya zama mai fada aji kan harkokin siyasar Gambia, duk da cigaba da tattara bayanan cin zarfin Bil adama da kuma almubazzaranci da dukiyar jama’a da akeyi domin kai shi kotun duniya.

Bayan kwashe shekaru 22 a karagar mulki, shugaba Adama Barrow ya kada Jammeh a zaben da akayi a shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.