Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Bikin shekaru 100 da haihuwar marigayi Nelson Mandela

Tsohon shugaban Amurka Barrack Obama, ya gabatar da jawabi na musamman kan cika shekaru 100 da haihuwar marigayi Nelson Mandela.Taron na yau talata a Afrika ta Kudu, dai shi ne mafi muhimmanci da Obama ya taka rawa a cikinsa, tun bayan sauka daga shugabancin Amurka.

Barrack Obama a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a Johannesburg na Afrika ta kudu
Barrack Obama a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a Johannesburg na Afrika ta kudu REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Daya daga cikin muhimman batutuwan da jawabin na Barrack Obama ya mayar da hankali kai, shi ne jan hankalin matasa da su ci jajirce wajen tabbatar da dorewar kyakkyawar koyarwar marigayi Nelson Mandela musamman kan yakar nuna wariyar launi.

Tsohon Shugaban Amurka Barrack Obama yaba ci gaba da cewa babu wanda aka haifa tare akidar tsanar wani saboda launin fatarsa, asalinsa ko kuma addininsa.

Obama a jawabinsa ya karasa da cewa ‘mutane suna koyar akida ce ta tsana ko cin zarafin waninsu, kuma in har mutane zasu iya koyar akidar tsana, to kenan za a iya koya musu son juna, saboda soyayya ita ce tafi dacewa a hallice .

Mu rike wannan gaskiya, saboda nan da shekaru 100 masu zuwa, al’ummar wannan lokaci zasu yaba mana kan yadda muka jajirce wajen dorewar kyakkyawar akida.

Akalla mutane dubu 15,000 ne suka samu halartar taron bikin tunawa da ranar haihuwar ta Mandela a birnin Johannesburg.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.