Isa ga babban shafi
Obama-Kenya

Obama na ziyarar kaddamar da wasu ayyuka a Kenya

Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya fara ziyara a kasar Kenya inda zai kaddamar da wata Cibiyar horar da matasa. Da isar sa kasar a jiya, Obama ya gana da shugaba Uhuru Kenyatta da shugaban yan adawa Raila Odinga, kafin yau da safe ya tashi zuwa kauyen kakannin sa cikin matakan tsaro.

Da isarsa birnin Nairobi kafin karasawa kauyen Kolegu, Barrack Obama ya kira ilahirin al'ummar kasar ta Kenya 'yan uwansa.
Da isarsa birnin Nairobi kafin karasawa kauyen Kolegu, Barrack Obama ya kira ilahirin al'ummar kasar ta Kenya 'yan uwansa. REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Wannan dai ce ziyarar farko da Obama ke kai wa Kenya wadda ke matsayin mahaifar iyayenshi tun bayan ta 2015 wadda jirginsa ya gaza sauka a yammacin birnin Kisumu saboda da girmansa.

Ziyarar ta Obama a yau, za ta kai ga kaddamar da wasu ayyukan ci gaban matasa da 'yar uwarsa ta jini Auma Obama ta samar a kasar.

Obama ya ce yana tuna ziyararsa a kauyen na su na Kogelu lokacin yana da shekaru 27 da haihuwa, acewarsa ya tuna lokacin da suka sauka a Nairobi kafin daga bisani su hau jirgin kasa kana kuma motar safa daga baya kafin isa gidan Mama Sarah.

A cewarsa gudunmawar ta Auma Obama ga matasan Kenya abin alfahari ne gareshi ganin yadda 'yar uwar tasa ta damu da damuwar al'ummar kasarta.

Kauyen na Kolegu wanda shi ne asalin Obama a nan aka haifi mahaifinshi da kakanshi haka zalika a nan aka binne su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.