Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 19/10 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 20/10 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 20/10 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 19/10 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 19/10 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 20/10 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 20/10 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 19/10 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 20/10 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 19/10 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 20/10 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 20/10 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 19/10 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 20/10 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 19/10 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 19/10 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 20/10 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 20/10 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 19/10 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Gaggauce

Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a arewacin Najeriya ya sanar da ficewa daga Jam'iyyar APC mai mulkin kasar.
Sani wanda ya mika takaddar ficewa daga Jam'iyyar ga shugabanta na kasa Adams Oshimole bai sanar da dalilin ficewarsa ba, haka zalika bai fadi Jam'iyyar da zai koma ba.

Afrika

Osinbajo na ziyarar jaje a jihar Katsina

media Kimanin gidaje 200 suka rushe a ambaliyar jihar Katsina rfihausa

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci Katsina don jajanta wa al'ummar jihar bisa ibtila'in ambaliyar ruwa da ya hallaka mutane kimanin 50, yayin da gidaje sama da 200 suka rushe, lamarin da ya raba dubban mutane da muhallansu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa kan aukuwar lamarin, in da gwamnatinsa ta yi alkawarin taimaka wa wadanda abin ya shafa.

Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina Aminu Waziri, ya ce an samu ibtila'in ne  a karamar hukumar Jibia sakamakon ruwan da aka tafka a ranar Lahadi a garuruwan Tundun Tikari da Dan Tudu da Unguwar Kwakwa da Unguwar Mai Kwari.

Rahotanni na cewa, ambaliyar ta kora gawarwakin mutane har cikin Jamhuriyar Nijar,  yayin da tuni aka yi jana'izar wadanda suka rasa rayukansu.

Jami’in ya ce ruwan ya kuma lalata gonakai da dama baya ga kashe daruruwan dabbobi.

Shugaban hukumar agajin gaggawan ya ce tuni aka tura jami’an agajin gaggawa domin taimakawa mutanen da yankin da abin ya faru.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure