Isa ga babban shafi

Bemba zai tsaya takarar shugabancin Jamhuriyar Congo

Jam’iyyar adawa da MLC a Jamhuriyar Congo, ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasar Jean Pierre Bemba, a matsayin dan takarar ta a zaben shugabancin kasar, makawani kadan bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta wanke shi daga zargin aikata laifukan yaki a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo Jean-Pierre Bemba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo Jean-Pierre Bemba. Reuters
Talla

Takarar dai ka ‘iya zama babban kalubale ga gwamnatin shugaba Joseph Kabila, wanda ‘yan adawa ke zargin yana da aniyar sake tsayawa takara a zaben kasar na watan Disamba mai zuwa, bayan kin sauka daga mukaminsa da ya yi, duk kuwa da cewa wa’adinsa ya kare tun a shekarar da ta gabata.

Kin saukar Kabila da ke shugabantar Jamhuriyar Congo tun daga shekarar 2001 ya haddasa jerin zanga-zanga a kasar, da sukai sanadin hallakar rayukan 'yan kasar da dama da ke neman tilastawa shugaban yin murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.