Isa ga babban shafi
Kamaru

Kamaru: Hoton bidiyon kisan fararen hula ya haifar da ce-ce-ku-ce

Shugabanni da kungiyoyin kare hakkin dan adam na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan, wani hoton Bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta na Intanet, da ke nuna yadda wasu sanye da kakin sojin Kamaru, suka harbe wasu mata biyu da kananan yara ciki harda jinjiri.

Wasu jami'an sojin Kamaru da ke sintiri a wasu daga cikin yankunan da ke fama da rikicin Boko Haram, da ke kan iyaka da Najeriya.
Wasu jami'an sojin Kamaru da ke sintiri a wasu daga cikin yankunan da ke fama da rikicin Boko Haram, da ke kan iyaka da Najeriya. RFI/OR
Talla

Cikin Bidiyon mai tsawon kusan minti uku, an ga mata biyu, daya na rike da karamar yarinya, dayar kuwa dauke da jariri a bayanta.

Ko wanne daga cikin matan biyu na tare da rakiyar wasu mutane biyu sanye da kakin soji, rike da bindiga.

Bidiyon na nuna yadda daya mutumin lokuta da dama yake marin daya matar.

Wannan hoton Bidiyon dake nuna alamar an dauke shine da wayar hannu, inda mai daukar cikin harshen Faransanci yake bayani kai tsaye, tare da kiran sunayen mutanen akai-akai

Bayan an daure musu fuskokin su a ka kuma tilasta su tsuguna, batare da bata lokaci ba suka harbe ‘yar karamar yarinyar a kai, sai kuma matan biyu a gadon baya harda dan jaririn dake goye.

A cewar babbar jami’a a kungiyar kare hakkin bil’adama ta nahiyar Afirka REDHAC, Maximilienne Ngo Mbe, wannan hoton bidiyon, lallai dakarun tsaron Kamaru ne, kuma yankin Arewa mai nisa ne, inda sosoji ke fafatawa da mayakan Boko-Haram, inda takira hukumomi da su gudanar da bincike tare da hukunta masu laifi.

Sai dai a nasu bangaren mahukuntan Kamaru, ta bakin Ministan yada labarai kuma kakakin gwamnati, Isa Chiroma Bakary, sun girgiza kwarai da wannan bidiyo, wanda yace sun soma bincike don gano sahihancin bidiyon.

Ministan wanda ya jaddada cewa ba a kai ga tabbatar da sahihancin wannan hoton bidiyon ba, ya ja hankali kan yiwuwar wasu ne sukai kokarin batawa dakarun kasar Kamaru suna don jawowa kasar kyama daga kasashen duniya.

Kafin aukuwar wannan lamari dai, kungiyoyin kare hakkin bil’adama daga ciki da wajen kasar ta Kamaru, musamman ma Amnesty International, sun sha zargin jami’an tsaron Kamaru da wuce gona da iri a yakin da suke yi da Boko haram da kuma ‘yan aware da ke neman ballewa daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.