Isa ga babban shafi
Libya-'Yancirani

'Yan cirani 100 sun nutse a tekun Mediterranean

Akalla 'yan cirani 100 ake kyautata zaton sun bace yanzu haka a gabar tekun Mediterranean bayan nutsewar jirgin da su ke ciki yau juma'a a kokarin su na tsallaka nahiyar Turai. Jami'an tsaron gabar teku a Libyan sun tabbatar da ceto mutane 14 daga cikin 'yan ciranin wadanda ruwa ya janyo su dab da birnin Tripoli.

Adadin 'yan ciranin da ke kwarara Nahiyar Turai ya karu ne a shekarar 2014 lokacin da rikicin kasar Libya ya tsananta inda fiye da yan kudun hijira 650,000 suka tsallake ta tsakiyar tekun Mediterranean a wannan lokacin.
Adadin 'yan ciranin da ke kwarara Nahiyar Turai ya karu ne a shekarar 2014 lokacin da rikicin kasar Libya ya tsananta inda fiye da yan kudun hijira 650,000 suka tsallake ta tsakiyar tekun Mediterranean a wannan lokacin. REUTERS
Talla

Babban jami'in hukumar da ke kula da tsaron gabar teku a Libyan ya ce sun kame wani jirgin ruwa da ke makare da 'yan cirani fiye da 200 a gabashin birnin Tripoli.

Kasar Libya dai ita ce ke a matsayin babbar hanyar yanke ga 'yan ciranin da son shiga Nahiyar turai daga Afrika don samun rayuwa mai inganci, inda da dama kan yi amfani da jiragen ruwa marasa inganci ta hannun masu fasakwabrin 'yan ciranin.

A lokuta da dama makamantan 'yan ciranin da ke bi ta tekun na Mediterranean kan rasa rayukansu a hanya koma su bace baki daya ko kuma su fada hannun bata gari masu safarar bil'adama.

Haka zalika 'yan ciranin da suka yi nasarar tsallakawa Turan da rayukansu, jami'an tsaro kan tsare koma a taso keyarsu zuwa Libya duk kuwa da bakar wahalar da suka sha.

Adadin 'yan ciranin da ke kwarara Nahiyar Turai ya karu ne a shekarar 2014 lokacin da rikicin kasar Libya ya tsananta inda fiye da yan kudun hijira 650,000 suka tsallake ta tsakiyar tekun Mediterranean a wannan lokacin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.