Isa ga babban shafi
Sudan-Sudan ta kudu

Yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Salva Kirr da Rieck Machar

Bangarori masu hamayya da juna a Sudan ta Kudu sun sanya hannu kan yarjejeniyar kawo karshen rikicin da kasar ta  share tsawon shekaru tana fama da shi tare da haddasa asarar rayukan jama’a.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da abokin hamayyarsa na siyasa Rieck Machar
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da abokin hamayyarsa na siyasa Rieck Machar © AFP
Talla

Karkashin wannan yarjejeniya, bangarorin biyu sun amince da tsagaita wuta a cikin kwanaki uku masu zuwa, sai kuma kafa gwamnatin hadin kan kasa a cikin watanni hudu, tare da gaggauta sakin fursunoni daga bangarorin biyu.

Yarjejeniyar wadda aka sanya wa hannu a birnin Khartum na kasar Sudan bayan share yini biyu ana tattaunawa tsakanin Salva Kiir da Rieck Machar, ana fatan za ta kawo karshen rikicin da ya yi sanadiyyar jefa milyoyin mutrane a cikin mumman hali na rayuwa.

Ministan harkokin wajen Sudan kasar da ta dauki nauyin wannan taro Al-Dierdiry Ahmed, ya ce yarjejeniya na a matsayin tukuici ga al’ummar Sudan ta Kudu.

A cikin makon da ya gabata ne Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa da ke gudun hijira a Afirka ta Kudu Rieck Machar, suka yi ganawar farko a birnin Adis Ababa na kasar Habasha domin warware wannan rikici.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.