Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

'Yan gudun hijirar Najeriya na cikin garari a wannan lokaci na damina

Dubban ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu a yankin arewa maso gabashin Najeriya yanzu haka na cikin hadarin fuskantar cutuka a dai dai lokacin da damuna ta fadi a yankin kuma su ke fuskantar karancin matsugunai.

Ko a makon da ya gabata wata kididdiga ta majalisar dinkin duniya ta nuna cewa akwai akalla ‘yan gudun hijira miliyan daya da dubu dari bakwai a jihar Borno da makwabtanta Adamawa da Yobe.
Ko a makon da ya gabata wata kididdiga ta majalisar dinkin duniya ta nuna cewa akwai akalla ‘yan gudun hijira miliyan daya da dubu dari bakwai a jihar Borno da makwabtanta Adamawa da Yobe. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Wani binciken hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta NRC ya nuna yadda fiye da mutane dubu 4 ke kwana a tsakar titi a garin Dikwa bayan da suke tserewa luguden wutar da sojin Najeriyar ke yi kan mayakan boko haram a garuruwansu.

Daraktan hukumar ta NRC a Najeriya Cheick Ba ya ce sun damu matuka da halin da al’umma ke ciki a garin na Dikwa mai nisan kilomita 92 daga Maiduguri.

A cewarsa akwai tarin yara da yanzu haka ke kwanan a titi ba tare da abin shimfida ko na rufa ba duk kuwa da ruwan saman da ake zabgawa,

Yanzu haka dai a cewar Mr Ba yaran na cikin hadarin kamuwa da cutukan zazzabin cizon saro amai da gudawa dama sauran cutuka masu alaka da sanyi ko rashin tsaftar muhalli.

Najeriyar wadda ke ikirarin nasara kan mayakan na Boko Haram na neman ilahirin ‘yan gudun hijirar da aka kakkabe mayakan na Boko Haram daga garuruwansu da su koma muhallansu, duk da cewa har yanzu dakarunta na ci gaba da aikin fatattakar mayakan.

Ko dai kungiyoyin jinkai a kasar na ganin har yanzu fa da sauran rina a kaba game da zaman lafiyar garuruwan da ke wajen birnin na Maiduguri.

Ko a makon da ya gabata wata kididdiga ta majalisar dinkin duniya ta nuna cewa akwai akalla ‘yan gudun hijira miliyan daya da dubu dari bakwai a jihar Borno da makwabtanta Adamawa da Yobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.