Isa ga babban shafi
Najeriya-Jos

Buhari ya umurci tura karin jami'an tsaro da makamai a jihar Filato

Shugaban Najeriya Muhammadu ya bada umurnin girke makaman atilare da jiragen sama da ke kai hari da kuma karin dakaru a Yankunan da ake samun tashin hankali da ke Jihar Plateau domin shawo kan matsalar da ta haifar da rasa dimbin rayuka.

Buhari wanda ya yi Allah wadai da tashin hankalin, ya bukaci shugabanni a matakai daban daban da su tashi tsaye wajen sauke nauyin da ke kan su.
Buhari wanda ya yi Allah wadai da tashin hankalin, ya bukaci shugabanni a matakai daban daban da su tashi tsaye wajen sauke nauyin da ke kan su. Reuters
Talla

Gwamnan Jihar Plateau Simon Lalong ya bayyana haka lokacin da shugaban ya ziyarci Jihar domin jajantawa al’ummar ta rasa rayukan da aka yi sakamakon tashin hankalin da aka samu a kananan hukumomin Barikin Ladi da Jos ta Kudu da Riyom.

Gwamna Lalon ya kuma bukaci kafa rundunar Yan Sandan kwantar da tarzoma a Barikin Ladi domin kai daukin gaggawa wuraren da ake samun tashin hankali.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummar Jihar da su kauda banbance banbancen dake tsakanin su domin ganin sun yi aikin gina kasa da kuma samar da zaman lafiya.

Buhari wanda ya yi Allah wadai da tashin hankalin, ya bukaci shugabanni a matakai daban daban da su tashi tsaye wajen sauke nauyin da ke kan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.