Isa ga babban shafi
Zimbabwe

'Yan adawa sun yi tir da yunkurin kashe shugaban Zimbabwe

‘Yan adawa a Zimbabwe sun yi tir da yunkurin halaka shugaban kasar, Emmerson Mnangagwa da aka yi a ranar Asabar da ta gabata a yayin gudanar da taron jami’iyyar Zanu-PF mai mulki a birnin Bulawayo.

Shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa da ya tsallake rijiya da baya a ranar Asabar
Shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa da ya tsallake rijiya da baya a ranar Asabar Tafadzwa Ufumeli/via REUTERS
Talla

Mai magana da yawun ‘yan adawar, kuma dan Majalisar Dattijan kasar, David Coltart ne ya bayyana haka yayin zantawa da Radio France International.

Mr. Coltart ya ce, "wannan abin tsoro ne sosai kasancewar tun bayan da aka yi wa tsohon shugaba Robert Mugabe juyin mulki a watan Nuwamban bara, kasar ta kasance cikin kwanciyar hankali, in da ake gudanar ga tarukan siyasa cikin kwanciyar hankali kafin a baya-bayan nan da aka yi yunkurin halaka shugaba Mnangagwa."

"Dole ne mu yi Allah- wadai da wannan tashin hankali, kuma muna fatan za a gudanar da bincike mai adalci domin bankado asirin dukkanin wadanda suka kitsa kai wannan hari" in ji Coltart.

Dan adawar ya kara da cewa, yana da kyau kuma dukkanin yan siyasarmu su hada kai wajen magance barkewar tashin hankali a wannan kasa.

Tuni shugaba Mnangagwa ya bada tabbacin gudanar da zaben kamar yadda aka shirya a ranar 30 ga watan gobe duk da wannan al'amari da ya faru na kokarin kashe shi.

Akalla mutane 41 ne suka jikkata bayan wata aukuwar wata fashewa a dai dai lokacin da shugaban ke shirin barin dandamali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.