Isa ga babban shafi
Najeriya-Ta'addanci

Osinbajo ya nuna damuwa da kisan mutane 86 a Plateau

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya nuna bacin ransa kan kashe-kashen da aka samu a jihar Plateau. Osinbajo wanda ke jawabi yayin ziyarar da ya kai jihar yau Litinin ya ce ya zama wajibi Al'ummar kasar su rungumi dabi'ar zaman lafiya.

Tuni gwamnatin jihar ta Pulato ta sanya dokar takaita zirga-zirga a wasu daga cikin sassan jihar.
Tuni gwamnatin jihar ta Pulato ta sanya dokar takaita zirga-zirga a wasu daga cikin sassan jihar. rfihausa
Talla

Ziyarar ta Osinbajo na zuwa bayan kazamin tashin hankalin da ya faru jiya Lahadi wanda ya haddasa mutuwar akalla mutane 86.

Tuni gwamnatin jihar ta Pulato ta sanya dokar takaita zirga-zirga a wasu daga cikin sassan jihar.

Mai Magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya ce hare-haren ya biyo bayan satar shanu da kuma kisan wasu Fulani Makiyaya kafin daga bisani batun ya koma na siyasa inda aka rika tare motocin mambobin jam'iyyar APC ana kashe su.

Sai dai mai magana shawarcin shugaban Najeriyar ya zu tsananta bincike kuma za su hukunta duk wanda aka samu da hannu a haddasa rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.