Isa ga babban shafi
Nijar-MDD

Nijar ta fara daukar matakan kaucewa Ambaliyar ruwa

Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta fara daukar matakan ganin ta kaucewa hasashen fuskantar ambaliyar Ruwa a Daminar Bana. Majalisar Dinkin Duniya ce dai ta gargadi kasar kan yiwuwar fuskantar Ambaliyar ruwan a bana a dai dai lokacin da damuna ke faduwa a yankin yammacin Afrika.

Aikin inganta tabkunan don kaucewa ambaliyan ruwan zai rika sada ruwan da ke cikin tabkunan kai tsaye da kogin kwara ko isa Har zuwa tabakuna.
Aikin inganta tabkunan don kaucewa ambaliyan ruwan zai rika sada ruwan da ke cikin tabkunan kai tsaye da kogin kwara ko isa Har zuwa tabakuna. REUTERS/Tife Owolabi
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa za a iya samu mummunar ambaliyar ruwa a daminar bana cikin kasar ta Nijar wadda za ta iya shafar sama da mutane dubu 170 a sassan kasar.

To sai dai a cewar ministan kula da ayyukan jinkai na kasar Alhaji Lawan Magaji, yanzu haka gwamnati na cigaba daukar matakai domin tunkarar wannan matsala.

Ko a watan Afrilun da ya gabata, Gwamnatin ta Nijar ta dauki matakin inganta tabkunan da ke cikin manyan garuruwan kasar don ganin sun dauki adadin ruwan saman da za a fuskanta a bana.

Aikin inganta tabkunan don kaucewa ambaliyan ruwan zai rika sada ruwan da ke cikin tabkunan kai tsaye da kogin kwara ko isa Har zuwa tabakuna.

Ko a shekarar da ta gabata cikin watan Satumba, wata sanarwar ofishin bada agajin jinkai na majalisar dinkin duniya OCHA, ta nuna yadda ambaliyar ruwa ta jallaka mutane 54 bayan mutane 200,000 da suka rasa matsugunnasu a kasar ta Nijar.

Haka zalika ambaliyar ruwan a bara ta lalata akalla gidaje 11,000 ta kuma lalata fadin akalla kadada 12,000 na amfanin gona bayaga dabbobi 16,000 da suka salwanta musamman a biranen Yamai, Dosso, Tllaberi, Maradi da kuma Zandar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.