Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an tsaron Najeriya sun kame Kwamandojin IS biyu a Abuja

Jami’an tsaron farin kaya a Najeriya sun kame wasu kwamandojin tsagin kungiyar Boko Haram biyu da ke biyayya ga kungiyar IS wadanda ake zargi da shirya kai wasu muggan hare-haren ta’addanci a kasar.

Jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya.
Jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya. guardian.ng
Talla

Hukumar tsaron sirri ta farin kaya a Najeriyar DSS, cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da kwanan watan 21 ga watan Yunin 2018 ta ce ta yi nasarar kame kwamandojin na kungiyar IS a yammacin Afrika ne ranar 5 ga watan Mayu a wajen Abuja babban birnin Kasar.

Sanarwar ta nuna cewa Kwamandojin na IS a Yammacin Afrika kungiyar da aka fi sani da ISWA, na shirin hada hannu da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a Najeriyar wajen kai hare-hare kan mutanen da basu-ji-ba basu-gani-ba.

Haka zalika hukumar tsaron ta DSS ta ce ta kuma kame wasu mambobin kungiyar boko Haram 4 ciki har da kwararru ta fuskar hada bama-bamai.

Kamen dai na zuwa ne bayan wani rahoton jaridar Birtaniya da ya yi nuni da cewa, akwai tarin mayakan IS da ke neman damar shiga Najeriyar don kai hare-haren ta’addanci bayan fatattakarsu daga kasashen Iraqi da Syria.

Najeriyar wadda ke fuskantar matsalar tsaro, yanzu haka hare-haren ta’addancin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar ya hallaka fiye da mutane dubu 20 daga shekarar 2009 zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.