Bakonmu a Yau
Hajiya Nuratu Batagaraw kan barazanar shigowar mayakan ISIL Najeriya dama ziyarar ministan tsaron Sahel a kasar
Wallafawa ranar:
Kunna - 02:57
Najeriya za ta karbi bakuncin Ministocin Tsaron Kasashen yankin Sahel, a wani yunkuri na lalubo hanyoyin da Kasashen zasu bi wajen samar da zaman lafiya a cikinsu. Sakamkon yawaitar ‘yan ta’adda a yankin. Wakilinmu Muhammadu Kabiru Yusuf ya samu zantawa da Sakatariyar dindindin ta Ma’aikatar Tsaron Kasar, Hajiya Nuratu Batagaraw wacce ta wakilci Ministan tsaron Kasar a wajen taron, inda ta yi bayanin abinda taron zai fi mayar da hankali da ma barazanar da ake cewar yan kungiyar nan ta ISIS na shirin shigo da ‘ya’yanta cikin Najeriyar.