shagulgulan Sallar Idil Fitr a Najeriya
A Najeriya Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci karkashin jagorancin mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, ita ce ta tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a jihohi da dama na kasar a yammacin jiya.
Ko baya ga Najeriya, a yau ana gudanar da bukukuwan sallar a mafi yawan kasashen muslumi da suka hada da Chadi, Kamaru, Ghana, Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larawaba da dai sauransu.