Ministan harkokin wajen Belgium Didier Reynders ya ce Bemba wanda tuni iyalensa ke zaune a kasar za a karbe shi, to sai dai ya ce Belgium za ta cigaba da bai wa kotun hadin-kai a game da duk wasu batutuwa da suka shafi tsohon madugun ‘yan tawayen MLC.
A makon da ya gabata ne kotun hukkunta masu manyan laifuka ta duniya ICC, ta soke hukuncin daurin shekaru 18 da ta yankewa tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo Jean-Pierre Bemba, bisa aikata laifukan yaki.