Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara

'Yan bindiga sun kara kai farmaki kauyukan Zamfara

Wasu ‘yan bindida da ake kyautata zaton barayin shanu sun kai farmaki kan wasu kauyuka a Jihar Zamfara tare da sake hallaka tarin jama'a. Hare-haren 'Yan bindigar na zuwa ne kwana guda bayan rundunar Sojin saman kasar ta yi shelar kaddamar da wani shiri na musamman da ke da nufin dakile karancin tsaron da jihar ke fuskanta.

Ko a jiya Laraba rundunar sojin saman Najeriya ta aike da wasu jirage masu saukar Ungulu biyu ga dakarunta da ke jihar ta Zamfara wanda ta ce zai taimaka musu ta hanyar yin shawagi a sararin samnaiya da nufin gano 'yan Bindigar.
Ko a jiya Laraba rundunar sojin saman Najeriya ta aike da wasu jirage masu saukar Ungulu biyu ga dakarunta da ke jihar ta Zamfara wanda ta ce zai taimaka musu ta hanyar yin shawagi a sararin samnaiya da nufin gano 'yan Bindigar. shakarasquare
Talla

Kawo yanzu dai babu adadin mutanen da harin ya hallaka sai dai rahotanni na nuni da cewa al'ummar kauyukan na ci gaba da tserewa don samun mafaka a biranen jihar, a dai dai lokacin da adadin 'yan wadanda ke kauracewa gidajen na su ya tasamma dubu 10.

Hare-haren 'yan bindigar kan kauyuka a Jihar ta Zamfara na matsayin ruwan dare wanda kuma a lokuta da dama ke hallaka tarin rayuka duk da cewa hukumomi na ikirarin daukar matakan gaggawa.

Harin na yau, na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan jihar ke sanar da wani harin baya-bayan nan da ya hallaka akalla mutane 10, a kauyukan Dutsen-Wake da Oho a karamar hukumar Birnin-Magaji.

Kakakin rundunar 'Yansandan jihar Zamfara DSP Muhammad Shehu a wani taron manema labarai da ya kira yau din nan ya ce ‘yan bindigar sun kai hare-haren kan kauyukan da misalin karfe 10 na dare a ranar Talatar da ta gabata.

Sai dai DSP Shehu, ya ce a lokacin da jami’an su suka kai wa al’ummar kauyukan dauki, maharan sun tsere zuwa cikin dajin Rugu, wanda ya yi iyaka da jihar ta Zamfara da Katsina.

Ko a jiya Laraba rundunar sojin saman Najeriya ta aike da wasu jirage masu saukar Ungulu biyu ga dakarunta da ke jihar ta Zamfara wanda ta ce zai taimaka musu ta hanyar yin shawagi a sararin samnaiya da nufin gano 'yan Bindigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.