Isa ga babban shafi
Morocco-wasanni

Morocco ta rasa damar karbar bakoncin gasar cin kofin duniya

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta amince da bai wa kasashen Amurka Canada da kuma Mexico damar karbar bakoncin gasar cin kofin duniya ta 2026 bayan kudirin da suka shigar da ya doke wanda Morocco ta gabatar.

Akwai dai kwara-ran zarge-zarge na cewa kasashe na biyan mambobin hukumar FIFA makudan kudade don kada musu kuri'ar karbar bakoncin gasar cin kofin duniyar.
Akwai dai kwara-ran zarge-zarge na cewa kasashe na biyan mambobin hukumar FIFA makudan kudade don kada musu kuri'ar karbar bakoncin gasar cin kofin duniyar. REUTERS/Arnd Wiegmann/Files
Talla

Mambobin hukumar ta FIFA ne dai suka kada kuri’a ga bangarorin biyu inda Amurka da Mexico da kuma Canada suka samu jumullar kuri’u 134 yayinda Morocco ta samu 65.

Ana ganin gasar cin kofin duniyar ta 2026 zata kasance mafi girma da kayatarwa da aka taba fuskanta a Tarihi, inda za a samu wakilcin kasashe 48 a kuma yi karawa 80 a tsawon kwanaki 34.

Tun farko dai Morocco ce ta fara mika bukatar karbarbar bakoncin a 2026 wanda kuma shi ne karo na 3 da ta ke neman karbar bakoncin gasar cin kofin duniyar amma kuma daga bisani kasashen Amurkan Canada da kuma Mexico suka zamo mata cikas.

Mambobin FIFA 211 daga mabanbantan kasashe ne suka yi zaman tantance kuri’un yau Laraba a Rasha yayinda Ghana ta kauracewa zaman kan abin da ta magudi.

Mexico dai ta taba karbar bakoncin gasar cin kofin duniyar a 1970 da 1986 haka zalika Amurka a 1994 yayinda kuma Canada ta karbi bangaren mata a 2015.

Akwai dai zarge-zargen cewa kasashe na biya mambobin hukumar don kada musu kuri’ar nasarar karbar gasar cin kofin duniyar kamar dai yadda ya faru a 2010 lokacin da FIFA ta amince da Rasha ta karbi gasar cin kofin duniya a 2018 ita kuma Qatar ta karba a 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.