Isa ga babban shafi
Sahel

Fiye da mutane miliyan 6 na fuskantar tsananin yunwa a Sahel - MDD

Shugaban hukumar Jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya, Mark Lowcock, ya yi gargadin cewar ana fuskantar matsalar samar da abinci a yankin Sahel wanda ke nuna karuwar mutanen da ke fuskantar matsalar abinci mai gina jiki irin sa na farko tun bayan shekarar 2012.

Wasu daga cikin yara masu fama da karancin abinci a yankin Sahel
Wasu daga cikin yara masu fama da karancin abinci a yankin Sahel Wikipedia
Talla

Jami’in ya ce akalla kusan mutane milyan 6 ne ke shan wahala wajen samawa kan su abinda za su ci a kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da Nijar da kuma Senegal, inda yara sama da milyan guda da rabi ke fama da tamowa.

Lowcock ya ce yanzu haka milyoyin mutane sun cinye dan abincin da suka yi tanadi, yayin da wasu suka fara rage yawan abincin da suke ci a rana da kuma janye yaran su daga makarantu.

Jami’in ya kuma ce matsalar rashin abincin ya karu da kashi 50, yayin da kowanne yaro guda daga yara 6 ke bukatar kulawa ta musamman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.