Isa ga babban shafi
Congo Dimokuradiyya

Shugaba Joseph Kabila ba zai tsaya takarar zaben kasar ba

Gwamnatin kasar Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo ta ce shugaba Joseph Kabila ba zai tsaya takarar neman wa’adi na uku  a zaben kasar da za’ayi a watan Disamba mai zuwa ba.

Joseph Kabila,Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo
Joseph Kabila,Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Firaministan kasar Bruno Tshibala ya bayyana haka saboda tanadin kundin tsarin mulki da ya hana shi takara.

Firaministan yace zaben da aka shirya gudanarwa ranar 23 ga watan Disamba zai gudana ba tare da wani tarnaki ba.

Wa’adin shugaba Kabila ya kare ne tun a shekarar 2016 amma yaki sauka a yunkurin da ake cewa zai sake takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.