Gwamnatin Najeriya ta shirya wani gagarumin biki domin karrama marigayi Chief MKO Abiola tare da mataimakin sa Amb Babagana Kingibe da ake hasashen su suka lashe zaben 12 ga watan Yuni shekarar 1993, yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokradiya.
Tuni matakin na sa ya haifar da cece kuce daga bangarori daban daban ciki harda masu adawa da bukatar sanar da sakamakon wancan zaben da kuma fargabar abinda zai haifar.
Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Tsohon Gwamnan Jihar Filato na wancan lokaci a karkashin Jam’iyyar SDP da Abiola ya tsaya a tutar ta, wato Ambasada Fidelis Tapgun, kuma ga abinda yake cewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu