Yan adawa sun gudanar da zanga-zanga a Bamako
Yan adawa sun fito a jiya juma’a a babban birnin Bamako na kasar Mali domin tilasatawa Gwamnatin kasar daukar alkawali na shirya sahihin zaben shugaban kasa na ranar 29 ga watan yulin shekarar nan da muke ciki.
Wallafawa ranar:
Domin kaucewa sake fuskantar tashin hankali hukumomi a Bamako sun aike da jami’an tsaro da suka tabbatar da tsaro a lokacin wannan zanga-zanga.
Yan adawan dauke da sakonni inda ake iya karanta cewa sahihi zabe demokuradiyya kenan, sun bukaci Shugaban kasar Ibrahim Bubacar Keita da ya nisan ta kan sa daga abinda yan adawa ke kira kokarin kawo cikas ga demokuradiyyar kasar Mali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu