Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun kai farmaki kauyuka 7 a jihar Zamfara

Rahotanni daga Jihar Zamfara da ke Najeriya sun ce akalla kauyuka 7 'Yan bindigar da ke satar shanu suka afkawa a yammacin jiya, inda suka tilastawa mazaunan su tserewa zuwa garin Mada domin samun mafaka.

Mutanen da suka tserewa 'yan bindiga kenan daga wasu kauyuka 7 na jihar Zamfara, inda yanzu su ke samun mafaka a garin Mada.
Mutanen da suka tserewa 'yan bindiga kenan daga wasu kauyuka 7 na jihar Zamfara, inda yanzu su ke samun mafaka a garin Mada. rfihausa
Talla

A daidai lokacin da gwamnatin Najeriyar ke shirin tura karin jami’an tsaro 2,000 zuwa Zamfara domin samar da tsaro, Barayin shanun a yammacin jiya sun sake afkawa wasu kauyuka har guda 7 inda suka bude wuta a dai dai lokacin da jama’a ke buda baki bayan kai Azumi.

Musa Kalla daga Fura-girke na daya daga cikin wadanda suka tsira da rayukan su, wanda ya ce yanzu haka suna samun mafaka a wata makaranta da ke garin Mada.

A cewar Musa Kalla 'yan bindigar sun kashe mutane da dama a garuruwan bakwai da suka hadar da Fura-girke da Wonaka da gidan mai daka da kuma dunkulawa yayinda suka yi awon gaba da tarin dabbobinsu.

Bala Yaro Mada, mazaunin garin na Mada ne inda mutanen kauyukan 7 yanzu haka suka samu mafaka, ya ce yanzu haka an bai wa jama'ar matsugunai a makarantu, tare da 'yan tsirarun dabbobin da suka tsira dasu daga hannun 'yan bindigar.

Sufeto Janar an Yan Sandan Najeriya Ibrahim Idris ya sha alwashin ganin bayan wadanan hare hare inda ya ce nan gaba kadan batun zai zamo tarihi.

Jihar zamfara dai ta shafe tsawon lokaci ta na fuskantar matsalar 'yan bindiga masu satar shanu kuma duk da yunkurin da gwamnati ke ikirarin yi na kawo karshen lamarin har yanzu al'amarin na fantsama zuwa wasu yankunan jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.