Isa ga babban shafi
Madagascar

Babban jami’in MDD ya zama Fira Ministan kasar Madagascar

A kasar Madagascar an zabi wani babban jami’in diplomasiyya na Majalisar dinkin Duniya a matsayin sabon Fira Ministan kasar.

Shugaban kasar Madagascar Hery Rajaonarimampianina.
Shugaban kasar Madagascar Hery Rajaonarimampianina. REUTERS/Lintao Zhang
Talla

Shugaban kasar Madagascar Hery Rajaonarimampianina ya sanar da sunan wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya don zamowa Fira ministan kasar da nufin kawo karshen boren da kasar ke fuskanta tun bayan samar da wasu sauye-sauye a tsarin zaben kasar.

Matakin shugaba Hery dai na zuwa ne a dai dai lokacin da zaben kasar ke kara karatowa.

A baya bayan nan ne dai kasar wadda ke gab da Tekun India ke ci gaba da fuskantar bore da zanga-zanga bayan shigar da wani kudurin doka kan tsarin zaben kasar, matakin da bangaren adawa ke ganin kokari ne na haramtawa dan takararsu yin takara a zaben kasar mai zuwa.

Yayin wani taron manema labarai da ya kira, shugaba Hery Rajao, ya bayyana sunan Christian Ntsay a matsayin sabon Fira ministan kasar, wanda ya ce ta haka ne za a warware rikicin da ake fuskanta.

A cewarsa Mr Christian yana da kwarewa tare da gogewar da zai hada kan al’ummar kasar, inda ya bukaci bangarorin siyasar kasar su girmama shi tare da bashi hadin kan da ya kamata.

Mr Christian mai shekaru 57, wanda a tarihi bai taba yin siyasa ba, amma kuma yana da gogewa wajen shugabantar kungiyoyin kwadago na duniya a matakai daban-daban, haka zalika ya rike mukamin ministan yawon bude ido na kasar tsakanin shekarun 2002 zuwa 2003.

Da safiyar litinin ne dai tsohon Firaministan kasar Mr Olivier Mahalafy ya sanar da murabus dinsa amma ya ce bai yi bankwana ba, don yana nan dawo wa nan gaba kadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.