Isa ga babban shafi
Mali

An yi arrangama tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaron Mali

Akalla mutane 16 ne suka jikkata a lokacin da ‘yan sandan kwantar da tarzoma na Mali sukai amfani da hayaki mai sa hawaye, wajen tarwatsa dandazon ‘yan adawa da ke yunkurin yin zanga-zanga a birnin Bamako, wadanda ke neman a gudanar da sahihin zaben shugaban kasa da za a yi wata mai kamawa.

'Yan sandan kwantar da tarzoma na Mali, yayin kokarin tarwatsa zanga-zangar 'yan adawa a birnin Bamako.
'Yan sandan kwantar da tarzoma na Mali, yayin kokarin tarwatsa zanga-zangar 'yan adawa a birnin Bamako. REUTERS/Idrissa Sangare
Talla

Shugaba mai ci Ibrahim Boubacar Kieta na daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar, inda zai nemi wa’adi na 2, duka ga zargin gwamnatinsa da gazawa wajen magance matsalar rashin aikin yi, da hare-haren ta’addanci, da kuma rikicin kabilanci musamman a arewacin kasar.

‘Yan takara 12 ne suka sanar da aniyar fafatawa a zaben shugaban kasar, ciki harda jagoran ‘yan adawa Souma’ila Cisse, tsohon ministan kudin kasar ta Mali.

Bayan da kura ta lafa a arrangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro, jagoran ‘yan adawa kuma dan takarar shugabancin kasar ta Mali, Souma’ila Cisse zasu ci gaba da fafutukar ganin kasar tabi kyakkyawan tsarin dimokaradiyya, ba tare da sun bari barazana ya yanke musu hanzari ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.