Isa ga babban shafi
Habasha

Habasha za ta dage dokar ta baci

Majalisar Habasha na shirin dage dokar ta bacin da aka ayyana a fadin kasar, watanni biyu kafin wa’adinta ya kare.

Sabon Fira Ministan Habasha, Abiy Ahmed a zauren majalisar kasar da ke birnin Addis Ababa.
Sabon Fira Ministan Habasha, Abiy Ahmed a zauren majalisar kasar da ke birnin Addis Ababa. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

A ranar litinin ake sa ran majalisar mai kujeru 547 zata kada kuri’a akan kudurin.

Matakin ya biyo bayan amincewar da majalisar zartaswar gwamnatin kasar ta yi da cewa a halin yanzu an samu zaman lafiya daga tashe,tashen hankulan da aka fuskanta a watanin baya.

A watan Fabarairu da ya gabata, gwamnatin Habasha ta ayyana dokar ta baci a fadin kasar, kwana guda bayan da Fira Minista Hailemariam Desalegn ya yi murabus, a dai dai lokacin da dubban ‘yan kasar ke zanga zangar adawa da gwamnati, musamman a yankin Oromiya, da yayi kaurin suna wajen adawar tun a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.