Masu safarar mutane sun hallaka bakin-haure a Libya
Majalisar Dinkin Duniya ta ce masu safarar mutane a Libya sun harbe wasu bakin- haure 12 har lahira, tare da jikkata wasu da dama, yayinda suka yi kokarin tsrewa daga sansanin da suka tsare su.
Wallafawa ranar:
Lamarin wanda ya auku a garin Bani walid da ke kudu maso gabashin Tripoli ya faru ne tun a ranar 23 ga watan Mayun da ya gabata, amma sai a baya bayan nan majalisar dinkin duniyar ta bayyana aukuwarsa.
Majalisar ta ce sansanin da bakin-hauren sukai yunkunrin tserwa ya kunshi ‘yan kasashen Eritrea, habasha da kuma Somalia, wadanda yawansu ya haura 200
Bincike ya nuna cewa gungun masu safarar mutane sun tafiyar da sansanoni akalla 20, wadanda cikinsu suke tsare da bakin-haure da ke fafutukar tafiya zuwa turai ko ta wane hali a garin na Bani Walid da ke kasar ta Libya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu