Isa ga babban shafi
Mali

Gwamnatin Mali ta amince da dokar yiwa 'yan tawaye afuwa

Gwamnatin Mali ta amince da fara aikin wata doka samar da zaman lafiya, ta zata bada damar yiwa ‘yan tawayen kasar Afuwa wadanda suka tada kayar baya a shekarar 2012, wanda ya basu damar kwace iko da yankin arewacin kasar a waccan lokaci.

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita.
Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita. AFP Photo/Michele CATTANI
Talla

Sanawar gwamnatin Mali ta ce a karkashin sabuwar dokar za a biya diyya ga wadanda rikicin tada kayar bayan ‘yan tawayen ya rista da su, yayinda kuma shirin afuwar zai shafi ‘yan tawayen da suka yi nadamar muggan hare-haren da suka kai.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam da dama, sun bukaci Fira Ministan Mali, Soumeylou Boubeye Maiga, da ya dakatar da fara aikin dokar yin afuwar, har sai kwamitocin bincike masu zaman kansu sun kammala gudanar da aikinsu na binciko wadanda suka tafka laifukan cin zarafin bil’adama a tsakanin ‘yan tawayen, domin fuskantar hukunci.

A watannin Maris da Afrilu na shekarar 2012 ne dai mayakan ‘yan tawayen Mali da ke alakanta kansu da kungiyar al-Qaeda suka kwace iko da yankin arewacin Mali, kafin daga bisani, sojin Faransa su jagoranci kawar da mayakan a shekarar 2013.

Sai dai cikin shekaru 2 da suka gabata zuwa yanzu, hare-haren ‘yan bindiga da Mali ke fama da shi ya bazu daga arewaci zuwa tsakiya da ma kudancin kasar, zalika hare-haren sun ketara kan iyakokin kasar ta Mali da kasashen Burkina Faso da jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.