Isa ga babban shafi
Duniya

Antonio Guterres ya karrama sojoji 129 da suka mutu

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya karrama sojoji 129 da suka mutu wajen aikin samar da zaman lafiya da lambar girma wajen wani biki da akayi a New York.

Antonio Guterres, Sakatary Majalisar Dinkin Duniya
Antonio Guterres, Sakatary Majalisar Dinkin Duniya MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Cikin wadanda aka karrama harda sojojin Najeriya guda 3 da suka hada da kanar Ali Suleiman da ya rasu a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Samanja Remmy Amakwe da ya rasu a Dafur da kuma Kolawole Shogaolu da ya rasu a Mali.

Najeriya ce kasa ta 41 da tafi bada gudumawar sojojin dake aikin samar da zaman lafiya a Duniya, kuma yanzu haka kasar na da sojoji da yan Sanda sama da 500 dake aiki a kasashen Sudan da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Haiti da Lebanon da Sudan ta kudu da kuma yammacin Sahara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.