Isa ga babban shafi
Najeriya

IIPOB ta bukaci Igbo su zauna gida don tunawa da ranar Biafra

Kungiyar IPOB da ke fafutukar kare maradun ‘yan kabilar Igbo tare da ballewar Biafra daga Najeriya, ta bukaci mazauna yankin da su zauna gidajensu a wannan laraba, domin tunawa da ranar shelanta ballewar yankin da kuma abubuwan da suka faru sakamakon yakin basasar kasar tsakanin 1967-1970.

Magoya bayan Ipob dauke da tutar Biafra, 28 ga watan mayun 2017 a Aba.
Magoya bayan Ipob dauke da tutar Biafra, 28 ga watan mayun 2017 a Aba. STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

A shekarar da ta gabata gwamnatin Najeriya ta ayyana kungiyar ta IPOB a matsayin ta ta’addanci sakamakon yadda take tayar da hankula da kuma karya dokokin kasar, sannan aka hana magoya bayanta gudanar da taruruka ko kuma gangami a duk fadin kasar.

Gwamnatin jihar Anambara daya daga cikin jihohi 5 da ke yankin na Kudu maso gabashin Najeriya, ta yi gargadin cewa za ta ladaftar da duk ma’aikacin da ya kaurace wa aikinsa a yau. 

A jihar Ebonyi kuwa, gwamnati ta ce duk dan kasuwar da ya karba wannan kira na kasancewa gida a wannan laraba, za ta karbe shagonsa, yayin da a sauran jihohi irinsu Abia, rundunar ‘yan sanda ta bai wa wadanda ke bukatar ci gaba da harkokinsu na kasuwanci tabbacin samun kariya daga jami’anta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.