Isa ga babban shafi
Mozambique

'Yan bindiga sun fille kan mutane 10 a Mozambique

Jami'an tsaro a Mozambique sun tabbatar da kisan wasu mutane 10 ta hanyar sare musu kai da ake zargin 'yan bindiga ne suka aikata a wani kauye da ke arewacin kasar. Rundunar 'yan sandan a kasar ta sha alwashin kame wadanda suka kai harin ko da dai kawo yanzu ba a kai ga gano kungiyar da ta kai harin ba.

Jami'an 'yan sandan Mozambique sun sha alwashin gano wadanda suka aikata kisan na mutane 10 ta hanyar fille musu kawuna.
Jami'an 'yan sandan Mozambique sun sha alwashin gano wadanda suka aikata kisan na mutane 10 ta hanyar fille musu kawuna. AFP
Talla

Harin wanda aka kai shi da safiyar yau hukumomi sun tabbatar da cewa Maharan sun yi amfani da takobi ne wajen fille kawunan har mutane 10.

Cikin wadanda aka fillewa kan inji rundunar 'yan sandan ta Mozambique har da wasu yara maza biyu da shekarunsu bai haura 15 zuwa 16 ba, wadanda aka aikesu don nemo kiraren girki don dafa musu kalacin safe.

Mai magana da yawun rundunar 'Yansandan kasar Inacio Dina yayin wani taron manema labarai kan kisan na Mutane 10 ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen lalubo wadanda suka aikata kisan tare da yi musu hukunci.

Kawo yanzu dai babu ko da mutum guda da rundunar ta kama bisa zargin kisan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.