Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko haram ta kashe mutane 4 a harin Bom din Kwanduga

Akalla mutane hudu sun mutu yayinda wasu bakwai kuma suka jikkata a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno, bayan wani hari da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram da kai wa gab da sansanin 'yan gudun hijira a yau Litinin.

Karamar hukumar kwanduga na daga cikin yankunan da ke ci gaba da fuskantar hare-haren ta’addanci daga kungiyar ta Boko Haram tun bayan bullowar kungiyar kusan shekaru 10.
Karamar hukumar kwanduga na daga cikin yankunan da ke ci gaba da fuskantar hare-haren ta’addanci daga kungiyar ta Boko Haram tun bayan bullowar kungiyar kusan shekaru 10. Guardian Nigeria
Talla

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar ha harin wanda ta ce ya hallaka mutane hudu da suka kunshi fararen hula biyu.

Kwamishinan ‘yan ta Damian Chuku wanda ke tabbatar da hakan ga manema labarai bai fayyace ainahin sauran mutane biyun da harin ya shafa ba.

Haka zalika ya bayyana cewa, dukkanin alamu sun nuna cewa maharan sun yi kokarin tayar da bom din ne a sansanin ‘yan gudun hijira amma tsaron da ke wajen yasa suka dasa shi a yankin Mashimari da ke gab da sansanin na Konduga

A cewarsa tuni aka aike da jami’an tsaro yankin kuma komai ya kammala dai daita.

Karamar hukumar kwanduga na daga cikin yankunan da ke ci gaba da fuskantar hare-haren ta’addanci daga kungiyar ta Boko Haram tun bayan bullowar kungiyar kusan shekaru 10.

Ko a ranar 17 ga watan Fabarairun shekarar nan sai da wani harin bom da kungiyar ta Boko Haram ta kai babbar kasuwar kifi ya hallaka fiye da mutane 22 baya ga jikkata wasu da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.