Isa ga babban shafi
Najeriya

Al'ummar Bodo dake Najeriya na murnar samun nasara a kotu

Al’ummar Bodo dake yankin Naija Delta dake Najeriya sun bayyana farin cikin su da nasarar da suka ce sun samu cikin shari’ar da suke yi da kamfanin hakar man Shell da suke zargi da lalata musu muhalli.

Wasu yankunan da Kamfanin Shell ke gudanar da hakar mai a Naija Delta
Wasu yankunan da Kamfanin Shell ke gudanar da hakar mai a Naija Delta AFP Photo/Pius Utomi Ekpei
Talla

Yayin yanke hukunci kan karar da al’ummar Bodo suka shigar a kotun dake London, mai shari’a Justice Cockerill tace ana iya cigaba da shari’ar ranar 1 ga watan Yulin shekara mai zuwa, sabanin bukatar kamfanin Shell na watsi da karar.

Mutanen Bodo sun shigar da karar ne inda suke bukatar kamfanin Shell ya tsaftace musu muhallin su da ya gurbata wajen aikin hakar mai sakamakon kwararar sa da aka samu.

A shekarar 2015 kamfanin Shell ya dauki alhakin aikata laifin, inda yayi alkawarin biyan dalla milyan 83 ga mazauna yankin da kuma tsaftace musu muhalli.

Tuni dai aka fara aikin tsaftace muhallin a karkashin gwamnatin Najeriya mai ci, amma mutanen Bodo na bukatar kotun ta sanya ido wajen tabbatar da cewar anyi aiki mai inganci wajen tsaftace musu muhallin.

Lauyan al’ummar Dan Leader ya bayyana farin cikin su da matsayin kotun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.