Isa ga babban shafi
Afrika

An karrama bankunan Afrika da suka yi fice

An gudanar da gagarumin bikin karrama bankunan Afrika da suka yi fice a fannoni da dama a birnin Busan na Korea ta Kudu. A bana dai, bankunan yankin gabashin Afrika ne suka mamaye kyautukan da aka bayar a bikin wanda aka gudanar a gefen taron bankin raye kasashen Afrika na shekara-shekara.

Gabashin Afrika ya mamaye kyautukar da ake bai wa bankunan da suka fi yin fice a fannoni da dama a bara
Gabashin Afrika ya mamaye kyautukar da ake bai wa bankunan da suka fi yin fice a fannoni da dama a bara kenyanwallstreet.com/
Talla

Shugaban rukunin bankin Equity na Kenya, James Mwangi ya lashe kyautar gwarzon ma’aikacin banki a bana, yayin da bankinsa ya samu habbaka ta hanyar bullo da wasu tsare-tsare da kuma fadada hanyoyin zuba jari.

Bankin na Equity ya kuma doke wasu bankuna hudu wajen lashe kyautar bankin da ya fi jajircewar cimma muradunsa.

Dr. Benno Ndulu na Tanzania, ya lashe gwarzon gwamnan babban bankin shekara a Afrika bisa aikinsa na tinzira zuba kudade da kuma samar da ingantaccen tsarin tafiyar da manyan harkokin bunkasa tattalin azriki.

Kazalika bankin CRDB na Tanzania ne ya zama gwarzo a yankin gabashin Afrika baki daya.

Bankin Standard na Afrika ta Kudu ya lashe kyautuka uku kai tsaye da suka hada da wadda ake bai wa bankin da ya fi fice wajen zuba jari .

Har ila yau bankin na Standard da kuma Merchant bank sun lashe kyauta a fannin kulla yarjejeniyar samar da kayayyakin more rayuwa. Bankunan biyu sun jagorancin cimma yarjejeniyar Dala biliyan 5 don gina layin dogo na Nacala da kuma tashar jiragen ruwa a Mozambique da Malawi.

Shi ma bankin Eco ba a bar shi a baya ba, in da ya zama gwarzo a fannin kirkire-kirkire da kuma saukake harka da kananan ‘yan kasuwa don fadada ayyukansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.