An fara yiwa jama'a rigakafin Ebola a Jamguriyar Congo
Jami’an lafiya Jamhuriyar Congo sun fara aikin baiwa jama’a rigakafin cutar Ebola, a yunkurin da ake na dakile sake bazuwar cutar zuwa sassan kasar. Cutar Ebolar dai na ci gaba da yaduwa a kasar duk da matakan da hukumomin ke dauka na ganin sun dakile ta.
Wallafawa ranar:
An dai taba amfani da maganin rigakafin a tsakanin shekarun 2014-2016, kuma an samu nasara a wancan lokacin.
Faran aikin rigakafin ya zo a dai dai lokacin da ma’aikatar lafiyar kasar ta sanar da karuwar wadanda suka hallaka a dalilin kamuwa da cutar zuwa 26 bayan mutuwar wata jami’ar jiyya.
Tuni dai kasashen Nahiyar Afrika suka fara daura damarar ganin sun kare al'ummarsu daga cutar ta Ebola mai hadarin gaske.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu