Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 06/12 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 01/12 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 01/12 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 06/12 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 01/12 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 06/12 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 01/12 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 06/12 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 01/12 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 06/12 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 01/12 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 06/12 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 01/12 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 01/12 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 06/12 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 01/12 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 06/12 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 01/12 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 06/12 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

'Yan shi'a sun jikkata 'yan sanda a Abuja

media Mabiya Shi'an dai sun yi ta jifan jami’an ‘yansandan da duwatsu inda su ke daga sauti kan lallai fa a saki jagoran na su Ibrahim Yakubu Zakzaky. REUTERS/Stringer

Wani dandazon mabiya Shi’a da ke zanga-zanga kan bukatar sakin jagoransu Ibrahim Yakubu Zakzaky da gwamnatin Najeriya ke ci gaba da tsare da shi kusan shekaru 3, sun farwa jami’an ‘yansandan da ke Sakateriyar gwamnatin Tarayya a Abuja babban birnin kasar.

Jami’an ‘yansandan dai sun yi yunkurin dakatar da mabiyan na Shi’a wadanda suka rika amfani da dutsuna wajen yin jifa baya ga tare hanyoyi da kuma yunkurin lalata motocin Jama’a.

Rahotanni sun ce mabiyan sun rufe manyan hanyoyin da za su sada jama’a da fadar gwamnatin kasar mai karancin tazara da sakatariyar matakin da ya tilasta ‘yansandan daukar mataki.

Mabiyan dai sun yi ta jifan jami’an ‘yansandan da duwatsu inda su ke daga sauti kan lallai fa a saki jagoran na su Ibrahim Yakubu Zakzaky.

Kamfanin dillacin labaran Najeriyar NAN ya ce tuni wasu jami’an ‘yansanda na musamman suka isa wajen bayan mabiya Shi’an sun raunata babban jami’in sashen kula da manyan laifuka na babbar Sakatariyar ‘yansandan lokacin da ya yi kokarin gabatar da jawabi garesu.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure