Isa ga babban shafi
wasanni

Babu tabbacin Enyeama zai shiga tawagar Super Eagles zuwa Rasha

A Najeriya har yanzu akwai fargabar ko fitaccen mai tsaron ragar kasar da ke taka leda a Club din Lille na faransa da ke buga lig 1 Vincent Enyeama zai amsa kirayen da kasar za ta yi masa don shiga cikin tawagarsa da za su wakilci kasar a gasar cin kofin duniya da za ta gudana a Rasha. 

Mai tsaron ragar Najeriya Vincent Enyeama tare da dan kwallon Argentina Lionel Messi.
Mai tsaron ragar Najeriya Vincent Enyeama tare da dan kwallon Argentina Lionel Messi. Pedro Ugarte/AFP
Talla

Vincent Enyeama dan shekaru 35 na a matsayin zabi daya tilo ga Najeriyar matukar tana fatan zuwa rashan da masu tsaron raga biyu don kaucewa fuskantar matsala.

Tuni dai aka fara gargadin mai horar da kungiyar kwallon kafar ta Najeriyar Gernot Rohr kan kada a maimaita kuskuren da kasar ta yi a gasar cin kofin duniya na shekarar 1998 da ya gudana a Faransa ta hanyar tafiya dan mai tsaron raga daya tilo.

Najeriyar dai a Faransa ta fuskanci lallasawa ta ci 4 da 1 daga Denmark sakamakon gajiyawar da mai tsaron ragarta Peter Rufa’I ya yi matakin da ya haddasa mata koma bayan da har yanzu ta ke dana sani akansa.

Kawo yanzu dai kasar na ci gaba da tattaro kan 'yan wasanta da ke taka leda a kungiyoyin kwallon kafar duniya da bayar da ta su gudunmawar a dai dai lokacin da ya rage kwanaki 31 a fara gasar ta cin kofin duniya da za ta samu halartar kasashe 32.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.