Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari na kan hanyar dawowa daga London a yau

Rahotanni daga fadar gwamnatin Najeriya na cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari zai isa babban birnin kasar Abuja da misalin karfe 7 na daren yau bayan shafe kwana uku a birnin London wajen ganin likitansa. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. NAN
Talla

Da farko dai an shirya cewa, Muhammadu Buhari zai shafe kwanaki hudu ne a birnin London don duba lafiyarsa amma kuma sanarwar da mukarraban shugaban suka fitar a dazun nan na nuni da cewa jirgin shugaban ya baro birnin London tun da misalin karfe 12 da rabi agogon Najeriya.

Ko a makon daya gabata ma dai shugaban ya tsaya a birnin London bayan barowarsa Amurka sakamakon matsalar da jirginsa ya fuskanta.

Kafin yanzu dai akwai jita-jitar da ke cewa babu tabbacin ranar dawowar shugaban wanda a bara ya shafe kusan watanni uku yana jinya.

Yanzu haka dai Muhammadu Buharin na fuskantar manyan kalubale, musamman bayan bayyana aniyarsa ta sake tsayawa shugabancin kasar a shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.